Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar (ADC), Atiku Abubakar, ya zargi wasu da ƙoƙarin hana shi shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ta hanyar amfani da rikicin shugabancin jam’iyyar wajen kawo cikas ga takararsa.
Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026.
A cikin sanarwar, Atiku ya danganta hukuncin kotun da ya shafi shugabancin Sanata David Mark da yunƙurin hana shi takara saboda kasancewarsa ɗan Arewa.
Ya yi zargin cewa waɗanda ke bayan wannan mataki sun yi amfani da Nafiu-Bala Gombe wajen ƙoƙarin amfani da kotu domin hana shi tsayawa takara. Sai dai ya jaddada cewa goyon bayan da yake samu ya wuce Arewacin Najeriya, yana mai cewa matsalolin tsadar rayuwa, ilimi da lafiya sun shafi ’yan Najeriya daga sassa daban-daban na ƙasar.
Haka kuma, Atiku ya nuna rashin amincewarsa da hukuncin, yana mai cewa Mai Shari’a Musa Liman na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya riga ya yanke hukunci kan shari’ar shugabancin David Mark mai lamba FHC/ABJ/CS/1637/2025.
Ya ce jam’iyyar ADC za ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar sabon hukuncin.
A ƙarshe, Atiku ya yi kira ga magoya bayan ADC da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da bin doka da oda tare da yaɗa saƙon jam’iyyar.
Ya kuma tabbatar da cewa yaƙin neman zaɓensu zai ci gaba a Kebbi da sauran sassan Najeriya.