Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane biyu masu fama da matsalar gani a ranar Litinin, a kan hanyar Riyom da ke ƙaramar hukumar Riyom ta Jihar Filato.
Masu garkuwar sun buƙaci a biya su kuɗin fansa naira miliyan 50.
Ishaya Ayuba Danjatau, mamba a Ƙungiyar Makafi ta Najeriya (Nigeria Association of the Blind), wadda waɗanda aka sace ɗin suke cikinta, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust da faruwar lamarin a safiyar ranar Talata.
A cewarsa, waɗanda aka sace ɗin na cikin tawagar masu buƙata ta musamman da suka taso daga Jihar Filato zuwa Jihar Benuwai domin halartar wani shiri da Gwamnan Jihar Benuwai ya shirya.
A cewar Danjatau, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Benuwai, sun samu labarin cewa an ɗage gudanar da shirin a kusa da Akwanga, inda daga bisani suka juya domin komawa Jos, amma abin takaici, masu garkuwa da mutane suka tare su a kusa da Riyom tare da yin awon gaba da su.
Ya ce: “Sun yanke shawarar komawa Jos maimakon ci gaba da tafiya bayan sun samu labarin cewa an ɗage shirin. A lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa, a kusa da ƙaramar hukumar Riyom, ne lamarin ya faru.
Shugaban Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙungiyoyin Masu Buƙata Ta Musamman ta Jihar Filato (JONAPWD), Shindol Aaron, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an yi garkuwa da mutanen ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare a ƙaramar hukumar Riyom.