NE

News Elementor

Daga Yanzu An daina Tattaunawa Da ‘Yan Bindiga Ko Biyan su Kudin Fansa A Najeriya – Janar Musa

Ministan tsaron Najeriya, General Christopher Musa mai ritaya, ya ce daga yanzu ba za a sake tattaunawa ko biyan kudin fansa ga yan ta’adda a kasar nan ba.

Ministan ya kuma bayyana cewa, ba za a kai karshen yaki da ta’addanci ba har sai lokacin da Najeriya ta samar da daftarin bayanan ‘yan kasa, wanda zai tattara bayanan al’ummar kasa a waje guda.

General Musa ya bayyana hakan ne a lokacin da majalisar dattawa ke tantance shi a matsayin sabon ministan tsaro na Kasa.

Lokacin da yake jawabi a gaban zauren majalisar, General Musa ya ce dole ne gwamnatoci a dukkanin matakai su haramta biyan kudin fansa ko tattaunawa da yan bindiga, domin kuwa yin hakan na karawa ‘yan bindigar karfi.

Ya ce za a iya sanya ido kan kudin fansar da ake biya, tare da cewa tsarin banki na kasar nan zai iya bibiyar dukkanin kudin da ake hada-hadarsu a bangaren ta’addanci.

Tsohon sojan ya jaddada cewa, kaso 25 zuwa 30 ne kadai sojojin da ake amfani da su wajan yaki da ta’addanci, inda ya kara da cewa, akwai matsaloli irin talauci, jahilci da raunin gwamnati dake taimakawa ayyukan ta’addanci a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM