Shugaban Amurika Donald Trump ya kulla yarjejeniyar zaman lafiya tare da shugabannin Rwanda da jamhuriyar dimukradiyyar Congo, a daidai lokacin da sabon rikici ya bulla a kasashen.
Trump ya ce Amurika za ta kulla yarjejeniya a bangaren ma’adinai tare da kasashen guda biyu, bayan ya karbi bakuncin shugaba Paul Kagame na Rwanda, da Felix Tshikedin na Congo a birnin Washington.
Da yake zantawa bayan kulla yarjejeniyar a cibiyar wanzar da zaman lafiya da aka sanyawa sunansa, shugaba Trump ya ce yarjejeniyar da suka kulla za ta bada mamaki sosai.
Ya ce shugabannin guda biyu sun shafe tsawon lokaci suna kisan suna, amma kuma a yanzu za su yi aiki tare da domin amfana da Amruika, kamar sauran kasashe.
To saidai, ana ganin samun jituwa a tsakanin shugabannin guda biyu zai yi wahala sosai, a yayin da rikici ya yi Kamari a gabaschin Congo inda kungiyar M23 da majalisar dunkin duniya ta ce na samun goyon bayan Rwanda, ke ci-gaba da samun galaba a kan dakarun Kinshasa.
Trump ya yi alfaharin cewa, rikicin na Congo, wanda ya yi sanadin mutuwar dubbanin mutane tsawon shekaru, na cikin yake-yake guda 8 da ya kai karshensu tun bayan da ya dawo kan mulkin Amurika a watan Junairu.