Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan rufe ofishin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da gwamnatin jihar Sokoto ta yi, bisa abin da ta bayyana a matsayin takaddamar mallakar ginin da ba ta da tushe.
Ƙungiyar ta ce rufe ofishin wani yunƙuri ne na gwamnatin jihar na danne ’yan adawa da kuma tauye ’yancin haɗuwa da ƙungiya, da kuma haƙƙin dukkan jam’iyyun siyasa na gudanar da ayyukansu cikin ’yanci.
Amnesty International ta bayyana cewa gwamnatin jihar Sokoto na nuna rashin damuwa da muhimman ƙa’idojin dimokuraɗiyya, ta hanyar amfani da ikon gwamnati wajen takaita harkokin siyasa, domin bai wa jam’iyyar da ke mulki wata dama ta hanyar da ba ta dace da doka ba.
Ƙungiyar ta ce amfani da dalilai kamar sake duba takardar shaidar mallakar filin ginin, wato Certificate of Occupancy, da sauran takardun da suka shafi ginin, domin halatta rufe ofishin ADC a Sokoto, na bayyana yunƙurin gwamnatin jihar na kawo cikas ga kasancewar jam’iyyun siyasa daban-daban a fagen siyasa.
Amnesty International ta ƙara da cewa wannan sabon mataki na gwamnatin jihar Sokoto ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wani rahoto da ya bayyana cewa an kai hari kan ayarin motocin ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar ADC, Hon. Manir Muhammad Dan’iya, kusa da filin jirgin saman Sultan Abubakar na III, a ranar Juma’a, 30 ga Oktoba.
Ƙungiyar ta ce maimakon hukumomin tsaro a jihar Sokoto su yi Allah-wadai da irin waɗannan abubuwa tare da kare haƙƙin jama’a, sun gaza sauke nauyin da ke kansu na tabbatar da bin doka da kuma kare haƙƙin kowa na gudanar da harkokin siyasa cikin lumana.
Ta kuma bayyana cewa yanayin fargaba da tsoratarwa da ake zargin ya mamaye jihar Sokoto na kawo cikas ga ’yancin taruwa da haɗuwa da ƙungiya.
Saboda haka, Amnesty International ta buƙaci hukumomin tsaro da su ɗauki matakan da suka dace domin dakile ci gaba da tabarbarewar haƙƙin bil’adama a jihar Sokoto, tare da tabbatar da cewa kowa na iya gudanar da harkokin siyasa cikin lumana da kuma ’yanci.