Takardun hukuncin kotu da aka tabbatar da sahihancinsu daga Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, sun tabbatar da cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta cire sunan ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Aminu Gwarzo, daga cikin jerin sunayen ’yan takarar da ta sabunta ne bisa biyayya ga umarnin kotu.
Ƙarar da ta jawo wannan mataki ta samo asali ne daga wasu ’ya’yan jam’iyyar NDC da ba su gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani na ɗan takarar gwamna ba, waɗanda suka haɗa da Garba Umar Isa, Yau Nasiru da Atiku Jamilu Abubakar.
Sun shigar da ƙarar ne a kan INEC a matsayin wanda ake ƙara na farko, da kuma jam’iyyar NDC a matsayin wadda ake ƙara ta biyu, ta hanyar neman umarnin kotu, a ranar 17 ga Oktoba, 2026.
Masu ƙarar dai ba su gamsu da yadda jagoran Kwankwasiyya, kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya tsayar da Aminu Gwarzo a matsayin ɗan takarar gwamna, tare da ɗansa Mustapha Kwankwaso a matsayin wanda zai yi masa mataimaki ba.
Jaridar Punch ta ce, a hukuncin da ya yanke ranar 27 ga Oktoba, 2026, Mai Shari’a Amobeda ya bayar da umarnin hana INEC, jami’anta, wakilanta ko duk wani mutum da ke aiki da ikonta, wallafa sunan kowane ɗan takara a cikin jerin sunayen ’yan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, har sai kotu ta kammala sauron buƙatar da aka gabatar mata.
Haka kuma, kotun ta bayar da umarnin hana INEC ko jami’anta yin wani sauyi, gyara, ƙari ko cire wani abu daga cikin jerin sunayen ’yan takarar gwamna na ƙarshe da hukumar ta wallafa a ranar 10 ga Oktoba, 2026, har sai an saurari buƙatar da aka gabatar wa kotun.
Matakin kotun ya ƙara bayyana dalilin da ya sa INEC ta ƙaurace wa saka sunan Aminu Gwarzo a cikin jerin sunayen ’yan takarar da ta sabunta, duk da ce-ce-ku-cen da aka samu kan batun takararsa.