NE

News Elementor

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan kallon masu sukar ta a matsayin makiya

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta daina kallon duk masu sukar manufofinta a matsayin makiyan Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta rika karɓar suka mai ma’ana.

Sanusi ya bayyana haka ne yayin wani taron shugabanci na Oxford Global Think Tank Leadership Conference da aka gudanar ta yanar gizo ranar Talata.

Ya ce bai kamata gwamnati ta ɗauki korafe-korafen jama’a kan talauci da tsadar rayuwa a matsayin suka gare ta ba, musamman a lokacin da al’umma ke fuskantar matsin tattalin arziki.

Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kuma nuna damuwa kan yawan kuɗin da gwamnati ke kashewa, yana mai cewa dole ne Najeriya ta tsara abubuwan da za ta ba fifiko, musamman a bangaren hanyoyi, wutar lantarki, noma da fasaha.

Sanusi ya bayyana cewa duk da sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu sun kawo ci gaba, inda ya ce haɓakar tattalin arziki ta tashi daga kashi 0.9 zuwa 4.5, yayin da hauhawar farashi ta ragu daga sama da kashi 30 zuwa 14.5, har yanzu akwai manyan matsaloli.

Ya ce ajiyar kuɗaɗen ƙasar waje ta Babban Bankin Najeriya ta kai dala biliyan 55, amma har yanzu talauci, yunwa, ƙarancin abinci mai gina jiki, mace-macen mata masu juna biyu da matsalolin ilimi da lafiya na ci gaba da addabar al’umma.

Sarkin ya kuma bukaci gwamnati ta magance matsalar ɗorewar bashin ƙasa, tare da samar da tallafin rage raɗaɗin sauye-sauyen tattalin arziki ga talakawa tun daga farko.

Ya ƙara da cewa dole ne gwamnati ta yi garambawul ga sauran fannoni, ba wai cire tallafin man fetur da sassauta farashin canjin kuɗi kawai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan kallon masu sukar ta a matsayin makiya

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta daina kallon duk masu sukar manufofinta a matsayin makiyan Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta rika karɓar suka mai ma’ana. Sanusi ya bayyana haka ne yayin wani taron shugabanci na Oxford Global Think Tank Leadership Conference da aka...

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM