NE

News Elementor

Atiku ya zargi wasu da koƙarin hana shi takarar shugaban kasa saboda shi dan Arewa ne

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar (ADC), Atiku Abubakar, ya zargi wasu da ƙoƙarin hana shi shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ta hanyar amfani da rikicin shugabancin jam’iyyar wajen kawo cikas ga takararsa.

Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026.

A cikin sanarwar, Atiku ya danganta hukuncin kotun da ya shafi shugabancin Sanata David Mark da yunƙurin hana shi takara saboda kasancewarsa ɗan Arewa.

Ya yi zargin cewa waɗanda ke bayan wannan mataki sun yi amfani da Nafiu-Bala Gombe wajen ƙoƙarin amfani da kotu domin hana shi tsayawa takara. Sai dai ya jaddada cewa goyon bayan da yake samu ya wuce Arewacin Najeriya, yana mai cewa matsalolin tsadar rayuwa, ilimi da lafiya sun shafi ’yan Najeriya daga sassa daban-daban na ƙasar.

Haka kuma, Atiku ya nuna rashin amincewarsa da hukuncin, yana mai cewa Mai Shari’a Musa Liman na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya riga ya yanke hukunci kan shari’ar shugabancin David Mark mai lamba FHC/ABJ/CS/1637/2025.

Ya ce jam’iyyar ADC za ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar sabon hukuncin.

A ƙarshe, Atiku ya yi kira ga magoya bayan ADC da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da bin doka da oda tare da yaɗa saƙon jam’iyyar.

Ya kuma tabbatar da cewa yaƙin neman zaɓensu zai ci gaba a Kebbi da sauran sassan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan kallon masu sukar ta a matsayin makiya

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta daina kallon duk masu sukar manufofinta a matsayin makiyan Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta rika karɓar suka mai ma’ana. Sanusi ya bayyana haka ne yayin wani taron shugabanci na Oxford Global Think Tank Leadership Conference da aka...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM