NE

News Elementor

Zargin kisan kiristoci: Amurka za ta saka takunkumi ga wasu a Najeriya

Amurka ta ce za ta saka takunkumi tare da hana biza ga duk wanda ta samu da hannu a zargin zaluntar Kiristoci a Najeriya.

Ministan harkokin waje na Amurka, Marco Rubio, ya bayyana a shafinsa na X cewa matakin martani ne ga abin da ya kira zaluntar Kiristoci, duk da cewa bai gabatar da hujjoji ba.

Ya ce:

“Amurka na ɗaukar mataki game da tashin hankali da zaluncin da ake yi wa Kiristoci a Najeriya da duniya baki ɗaya.”

Rubio ya ƙara da cewa ofishin harkokin wajen Amurka zai daina bayar da biza ga mutanen da ake zargi da tsara ko bada umarni ko ɗaukar nauyi wajen tauye haƙƙin yin addini.

Wannan mataki zai shafi Najeriya da sauran ƙasashen da ake zargin ana zaluntar mutane kan addini.

A ranar Laraba, wani kwamitin Majalisar Wakilan Amurka ya fitar da rahoto kan batun, inda wasu ‘yan majalisa suka maimaita ikirarin cewa ana kashe Kiristoci da gangan a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan kallon masu sukar ta a matsayin makiya

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta daina kallon duk masu sukar manufofinta a matsayin makiyan Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta rika karɓar suka mai ma’ana. Sanusi ya bayyana haka ne yayin wani taron shugabanci na Oxford Global Think Tank Leadership Conference da aka...

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM