NE

News Elementor

MURIC ta neman a dakatar da jarabawar Makarantar Koyon Aikin Lauya kan hana sanya hijabi

Kungiyar kare haƙƙin Musulmi ta MURIC, ta yi kira da a dakatar da jarabawar da ake gudanarwa a dukkan cibiyoyin Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Najeriya, sakamakon zargin cin zarafi, tsoratarwa da kuma hana ɗalibai mata Musulmi masu sanya hijabi shiga ɗakunan jarabawa.

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Musulunci ta kuma buƙaci gudanar da bincike kan abubuwan da suka faru, waɗanda rahotanni suka ce sun faru ne a lokacin jarabawar ƙarshe ta ɗaliban da ke neman samun shiga ƙungiyar lauyoyin Najeriya, a ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026.

MURIC ta yi gargaɗin cewa za ta tattara iyaye, matasan Musulmi da sauran masu ruwa da tsaki domin gudanar da zanga-zangar lumana a cibiyoyin Makarantar Koyon Aikin Lauya da ke faɗin ƙasar nan, idan ba a biya buƙatunta ba.

Kawo lokacin haɗa wannan rahoto, Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Najeriya ba ta mayar da martani kan zarge-zargen da aka yi mata ba.

Ƙungiyar ta bayyana matsayinta ne a cikin wata sanarwar manema labarai da wanda ya kafa ta kuma Babban Darakta, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar ranar Lahadi.

A cewar Akintola, an zargi hana wasu ɗalibai mata da ke sanye da hijabi shiga ɗakunan jarabawa a sassa daban-daban na ƙasar nan saboda tufafin da suka sanya na addininsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM