NE

News Elementor

Tinubu ya taya Sarkin Musulmi murnar cika shekaru 20 a kan karagar mulki

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, murnar cika shekaru 20 da hawa kan karagar mulki ta Daular Usmaniyya.

A cikin saƙon taya murnar da fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ta fitar a ranar Litinin, 2 ga Nuwamba, 2026, Shugaba Tinubu ya bi sahun miliyoyin ’yan Najeriya da sauran masu taya murna a faɗin duniya wajen murnar shekaru 20 na jagorancin Sarkin Musulmi.

Tinubu ya bayyana mulkin Sarkin Musulmi a matsayin mai tawali’u, jarumta da kuma cikakken sanin nauyin da ke kansa, yana mai cewa ya kiyaye tare da ƙarfafa al’adun daular Usmaniyya ta Sakkwato.

Shugaban ya ce Sarkin Musulmi ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da ci gaba, inda ya bayyana shi a matsayin jagoran ɗabi’u nagari, mai haɗa kan mabiya addinai daban-daban da kuma amintaccen mai ba shugabanni shawara a faɗin ƙasar nan.

Ya kuma yaba da gudunmawar Sarkin Musulmi ke bayarwa wajen inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai ta hanyar matsayinsa na Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin addinin Musulunci ta Najeriya, da kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Ƙasa kan Zaman Lafiya tsakanin Addinai.

A cewar Tinubu, jagorancin Sarkin Musulmi ya taimaka wajen samar da fahimtar juna tsakanin Kiristoci da Musulmi, tare da mayar da bambancin addini da al’adu na Najeriya a matsayin ƙarfin haɗin kai maimakon abin da ke haddasa rarrabuwar kai.

Shugaban ya ƙara da yaba wa Sarkin Musulmi kan ƙoƙarinsa na samar da zaman lafiya a Arewacin Najeriya da yankin Sahel, da kuma jajircewarsa wajen inganta ilimi, musamman ilimin ’ya’ya mata, jin daɗin manoma, lafiyar al’umma da tallafa wa masu rauni a cikin al’umma.

Tinubu ya kuma bayyana jin daɗinsa kan kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsa da Sarkin Musulmi, inda ya bayyana shawarwarinsa a matsayin masu gaskiya da kishin ƙasa, waɗanda a kodayaushe ake bayar da su bisa la’akari da muradun Najeriya.

Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba Sarkin Musulmi lafiya, tsawon rai da kuma ƙarin hikima, yana mai fatan mulkinsa zai ci gaba da inganta zaman lafiya a Sakkwato, haɗin kai a Najeriya da kuma kare muradun al’ummar Musulmi.

Shugaban ya kammala saƙonsa da sake taya Sarkin Musulmi murnar wannan gagarumar nasara mai cike da tarihi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM