Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya ce gwamnatin tarayya za ta yi aiki da jihar Imo domin bunkasa damarmakin zuba jari da ci-gaban tattalin arziki.
Lokacin da yake zantawa a babban taron tattalin arziki na jihar Imo a birnin Owerri, mataimakin shugaban kasa ya ce gwamnatin Tinubu za ta yi aiki da jihar domin tabbatar da cewa alumma sun amfana da shirye-shiryen samar da ci-gaba mai dorewa.
Shettima ya bayyana jihar Imo a matsayin babban ginshiki a kudurin Najeriya na fadada hanyoyin tattalin arziki, inda take da dimbin arziki a bangaren kimiyya, iskar gas, da kuma sarrafa kayan noma, kazalika da kanana da matsakaitan masana’antu.
Mataimakin shugaban kasar ya ce za a samar da ci-gaba a kasa ne kadai idan kowace jiha ta alkinta hanyoyinta na tattalin arziki.
Daga nan ya bukaci jihar Imo da ta rungumi fasahar kirkira domin samar da ci-gaba, inda ya ce a yanzu kasashen duniya na amfani da kimiyya da baiwar alumma, ba iya ma’adinan kasa ba.