Rundunar ƴansandan Jihar Zamfara ta ce ta kashe sama da ƴan bindiga 30 tare da dakile wani hari da suka yi yunkurin kai wa garin Bukkuyum da ke karamar hukumar Bukkuyum ta jihar.
Rundunar ta bayyana cewa ƴan bindigar sun yi yunkurin mamaye garin ne a ranar 28 ga Oktoba, 2026, amma jami’an ’yansanda tare da hadin gwiwar jami’an tsaron sa-kai sun fatattake su bayan musayar wuta mai zafi.
Kakakin rundunar ’yansandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Gusau ranar Asabar.
Ya ce jami’an tsaron sun nuna jarumtaka wajen kare garin, duk da karancin karfin makamai idan aka kwatanta da na ’yan bindigar.
A cewarsa, daga bisani an gano gawarwakin mutane sama da 30 da ake zargin ’yan bindigar ne a gonakin da ke kewayen garin, lamarin da ke nuna irin asarar da suka yi yayin arangamar.
Sai dai rundunar ta ce har yanzu ana ci gaba da tantance hakikanin adadin wadanda aka kashe.
Ta kara da cewa nasarar fatattakar ’yan bindigar ta hana asarar rayuka, lalata dukiyoyi da kuma tilasta wa mazauna yankin barin gidajensu.
Rundunar ta kuma ce matsin lambar da jami’an tsaro ke ci gaba da yi wa ’yan bindigar ya tilasta wa wasu daga cikinsu tserewa daga jihar.
Ta tabbatar da aniyar ci gaba da ayyukan kakkabe miyagun laifuka tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da dawo da kwanciyar hankalin al’umma.