Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nijeriya (EFCC), Mista Olanipekun Olukoyede, ya bayyana cewa Jihar Zamfara na samun sauyi a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, musamman a fannin gine-ginen ababen more rayuwa da ilimi.
Ya bayyana hakan ne yayin gabatar da babban jawabi a wajen bikin cika shekaru 30 da ƙirƙirar Jihar Zamfara, wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jiha da ke Gusau. DCL Hausa ta ruwaito cewa Mista Olukoyede ya ce ya gudanar da bincike kan jihar da kuma gwamnan kafin amincewa da gayyatar da aka yi masa na gabatar da jawabin bikin.
Ya ce abin da ya fara lura da shi bayan isa Gusau shi ne sabon filin jirgin sama, da sabbin hanyoyi da kuma fitilun hasken rana da aka girka a kan tituna.
Shugaban EFCC ya kuma bayyana cewa Zamfara na samun ci gaba a sakamakon gyare-gyaren da ake yi, inda ya yaba da yadda jihar ke inganta matsayinta a jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO.
Ya ce: “Zai ɗauki gwamna mai kishin dimokuraɗiyya, gaskiya da jajircewa kafin ya samu ƙarfin gayyatar Shugaban EFCC domin ya yi wa al’ummar jiharsa jawabi.”
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya ce taken bikin, ‘Tunani kan Abubuwan da Aka Cimma da Makomar Zamfara’, an zaɓe shi ne domin duba ƙalubalen da jihar ta fuskanta da kuma hanyoyin samar da kyakkyawar makoma.
Gwamnan ya bayyana cewa ajandar gyaran jihar guda shida da kuma shirin raya Zamfara na shekarar 2025 zuwa 2034 ne ke jagorantar manufofin gwamnatinsa a fannoni kamar tattalin arziki, ababen more rayuwa, ilimi da tsaro.