Kwamitin amintattu na jamiyyar PDP mai biyayya ga ministan birnin Abuja, Nyesom Wike, sun gudanar da taro na musamman domin dakile matsalolin da ke addabar jamiyyar.
Da yake gabatar da jawabin bude taron, shugaban kwamitin Mao Ohuabunwa, ya ce kwamitin ya himmatu wajan dawo da jamiyyar a hayyacinta tare da tabbatar da cewa an gudanar da zabukan shugabannin jamiyyar a matakin jihohi.
Ya shedawa wakillan kwamitin cewa sun shirya tsaf domin aiki tare da shugabannin jihohi domin samar da sabbin shugabanni a fadin kasar nan.
Sanata Ohuabunwa ya bayyana matakan da jamiyyar za ta dauka da suka kunshi zaben shugabannin jihohi, da kuma taimakawa wajan dawo da jamiyyar hayyacinta a matakin tarayya.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban jamiyyar, Abdulrahman Muhammad, da sakatarenta na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, da Philip Tanimu Aduda, da wasu shugabannin jamiyyar na jihohi hadi da yan majalisar tarayya.