Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai kai ziyarar aiki zuwa jihohi uku a cikin shirye-shiryen bukukuwan ƙarshen shekara.
A cewar wata sanarwa da hadimin shugaban kasar kan sha’anin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu zai bar Abuja a wannan Asabar domin kai ziyara a jihohin Borno, Bauchi da Legas.
A yayin ziyararsa a Jihar Borno, Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Babagana Zulum tare da Gwamnatin Tarayya suka aiwatar.
Haka kuma, zai halarci ɗaurin auren Sadiq Sheriff, ɗan tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Ali Modu Sheriff, da amaryarsa Hadiza Kam Salem.
Daga Maiduguri, Shugaban Ƙasar zai wuce zuwa Bauchi domin jajanta wa Gwamnatin Jihar Bauchi da kuma iyalan marigayi Sheikh Dahiru Bauchi, fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran ɗariƙar Tijjaniyya.
