Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa NDLEA reshen Jihar Sakkwato ta kama mutum 146 da ake zargi tare da ƙwace kilogiram 982.8 na miyagun ƙwayoyi a cikin watanni huɗu da suka gabata.
Kwamandan hukumar na jiha, Alhaji Mustapha Muhammad Gidado, ne ya bayyana hakan a yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan nasarorin da rundunar ta samu tun bayan da ya fara aiki watanni huɗu da suka gabata.
Gidado ya ce 13 daga cikin waɗanda aka kama, ciki har da wani dattijo mai shekaru 72, an riga an yanke musu hukunci, yayin da sauran 18 ke jira shari’a.
Ya ƙara da cewa rundunar ta yi gyran hali ga mutum 18 da ke fama da shaye-shayen ƙwayoyi, tare da mayar da su cikin iyalansu.
Gidado ya alakanta waɗannan nasarori da goyon bayan da suke samu daga Gwamnatin Jihar Sakkwato, haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, da kuma bayanan sirri da jama’ar ke ba jami’an hukumar cikin lokaci.