Tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, tare da ɗansa Abubakar Abdulaziz Malami, a yau, 2 ga Disamba, za su fara neman beli kan tuhumar cin hanci da rashawa ta Naira biliyan 9 da gwamnatin tarayya ta shigar a kansu.
Ana sa ran Malami, ɗansa, da wata Hajiya Bashir Asabe, ma’aikaciyar kamfanin Ramadiya Property Limited wadda a halin yanzu take tsare a gidan yari na Kuje bisa umarnin kotu, za a gurfanar da su a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja domin ci gaba da fafutukar neman beli daga inda ake tsare da su a gidan yarin Kuje.
