Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayar da umarnin sake buɗe dukkanin makarantu firamare da sakandare a faɗin jihar domin fara zangon karatu na biyu na shekarar karatu ta 2025/2026.
Umarnin zai fara aiki ne daga ranar Litinin, 5 ga Janairun, 2026.
Wannan na ƙunshe ne a cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Kebbi SUBEB, Isah Ibrahim, da Mataimakin Daraktan Ilimi, na Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta Jihar Kebbi, Aliyu Bagarawa, suka sanya wa hannu.
Sanarwar ta yi kira ga dukkan shugabannin makarantu, malamai, iyaye, ɗalibai da sakatarorin ilimi da su kula tare da tabbatar da bin umarnin yadda ya kamata.
An umurci shugabannin makarantu da su yi cikakkun shirye-shirye domin tabbatar da dawowa makarantu cikin kwanciyar hankali da sauƙin tafiyar da harkokin karatu.
Haka kuma, gwamnatin ta shawarci iyaye da masu kula da yara da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu da waɗanda suke kula da su sun koma makaranta cikin gaggawa.
