Wasu ƴanbindiga sun kashe fiye da mutum 30 a jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, bayan da suka kai mummunan hari a ƙauyen Demo. Bayanai sun nuna cewa maharan sun farmaki Kasuwan-Daji da yammacin ranar Asabar, inda suka ƙona kasuwar, suka lalata shaguna tare da sace kayan abinci da wasu mutane.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya ce ƴanbindigar da ake zargin sun fito ne daga dajin Kabe, kuma da safiyar Lahadi jami’an tsaro suka kai ziyara yankin bayan samun rahoton harin. A cewarsa, jami’an sun tarar da gawarwaki sama da mutum 30, tare da samun bayanan cewa an sace wasu mazauna yankin.
Rundunar tsaro ta tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike tare da ƙoƙarin ceto mutanen da aka sace. Jihar Neja na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da hare-haren ƴanbindiga, lamarin da ke ci gaba da tayar da hankalin al’umma.