NE

News Elementor

Gobara: Tinubu Ya Umarci Kashim Shettima Ya Ziyarci Kano

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Mataimakinsa, Kashim Shettima, da ya jagoranci babbar tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Kano domin jajanta wa ’yan kasuwar Singer bisa gobarar da ta lalata dukiyoyi a karshen mako.

Tawagar, wadda za ta tashi daga Abuja gobe, za ta isar da sakon ta’aziyyar Shugaban Kasa ga ’yan kasuwar da suka yi asarar biliyoyin Naira sakamakon gobarar, wadda ita ce ta biyu cikin makonni biyu a kasuwar.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa Tinubu, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Lahadi.

Acewar sanarwar, a madadin gwamnati, tawagar za ta kuma yi alkawarin bayar da tallafin kudi domin taimaka wa wadanda abin ya shafa tare da tallafa wa Jihar Kano wajen bude kasuwar cikin gaggawa.

Mambobin tawagar sun hada da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin; Sanata Kawu Ismaila; da dan majalisar wakilai Abubakar Kabir Bichi, shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar.

Haka kuma, Ministan Harkokin Jin Kai, Dakta Bernard M. Doro, da Darakta-Janar na hukumar NEMA, Zubaida Umar, na cikin tawagar.Shugaba Tinubu ya kuma yi waya da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ya mika ta’aziyyarsa ga ’yan kasuwa da al’ummar jihar bisa mummunar gobarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM