Ƙungiyar yaki da safarar kananan yara da bautar da su ta kasa NACTAL ta kafa kwamitin mutum bakwai domin yin cikakken nazari kan rahoton safarar mutane na shekarar 2025 da ma’akatar harkokin wajen Amurka ta fitar a kan Nigeria.
Kwamitin zai kuma shirya cikakkun bayanai da za su nuna gudunmawa, bayanai da ra’ayoyin ƙungiyoyin farar hula a Najeriya da abokan hulɗarsu.
Hakan na zuwa ne bayan da NACTAL ta lura cewa rahoton TIP na 2025, wanda ya sanya Najeriya a matsayi na biyu, bai yi cikakken bayyani ba kan tasirin ayyukan da ƙungiyoyin farar hula ke yi wajen yaƙi da wannan matsala a faɗin ƙasar nan.
NACTAL ta kuma yi kira ga Gwamnatin Najeriya da ta ƙara kaimi da jajircewa, ciki har da ƙara kuɗaɗen tallafi da kuma bayar da su a kan lokaci, domin magance yawaitar safarar mutane yadda ya kamata, tare da magance matsalolin talauci da rashin tsaro da ke haifar da cin zarafi da danniya.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar na ƙasa, Abdulganiyu Abubakar ya sanya wa hannu, hukumar ta ce tana nan daram kan aniyarta ta ci gaba da haɗin gwiwa da dukkanin masu ruwa da tsaki domin samar da ingantattun tsare-tsare, ƙarfafa aiki, da kuma tabbatar da dorewar ci gaba mai ma’ana wajen kawo ƙarshen safarar mutane, cin zarafi da kuma danniya a Najeriya.