NE

News Elementor

Nijeriya Ta Yi Gargaɗi Kan Haɗarin Kamuwa Da Sanƙarau A Wasu Jihohin Arewacin Ƙasar

Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta fitar da sanarwar gargaɗi game da lafiyar jama’a inda ta ce akwai jihohin arewacin ƙasar da dama da ke fuskantar ƙarin haɗarin kamuwa da cutar sankarau yayin da yanayin zafi ke ƙaruwa a sassan ƙasar.

A cikin wata sanarwa, hukumar ta bayyana cewa cutar sanƙarau wata mummunar cuta ce da ke shafar ƙwayoyin kariya da ke rufe ƙwaƙwalwa da lakar baya, kuma galibi ƙwayar cutar Neisseria meningitidis ce ke haddasa ta.

NiMet ta kuma bayyana cewa cutar na yaɗuwa ta hanyar numfashi daga mutum zuwa mutum, musamman a wuraren da ake cunkoso ko kuma wuraren da iska ba ta shiga yadda ya kamata.

Hukumar ta bayyana Sokoto, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kano, Jigawa, Adamawa, Gombe, Bauchi, Yobe da Borno a matsayin jihohin da ke cikin babban haɗari na kamuwa da cutar.

Ta kuma buƙaci mazauna yankunan tsakiyar ƙasar da su kasance cikin lura da alamun cutar tare da kai rahoton duk wani zargi kan alamomin cutar da wuri. A halin yanzu, Jihohin Filato, Oyo, Cross River, Edo, Ekiti da Enugu an sanya su cikin yankunan da ba sa ido sosai a kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM