NE

News Elementor

Ƙungiyar Kiristoci a Arewa da Bishof-Bishof sun ƙaryata ikirarin Trump na cewa sojin Amurka sun kawo ƙarshen kashe Kiristoci a Najeriya

Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya CA reshen jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya, tare da Bishof-Bishof na manyan choch-chochi, sun yi watsi da ikirarin Shugaban Amurka, Donald Trump, cewa sojojin Amurka ne suka kawo ƙarshen kashe Kiristoci a Najeriya.

Malaman addinin sun bayyana ikirarin Trump a matsayin mai yaudara, ƙarya kuma wanda bai yi daidai da halin da ake ciki a ƙasa ba, suna gargadin cewa irin wannan furuci na iya rage kokarin da ake yi wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro da ta daɗe tana addabar Najeriya.

Trump ya yi wannan furuci ne yayin wani taro da aka gudanar a birnin Washington ranar Juma’a, inda ya ce shigar Amurka cikin al’amuran Najeriya ta taka muhimmiyar rawa wajen dakatar da hare-haren da ake zargin an fi kai wa al’ummomin Kiristoci, musamman a yankunan da ke fama da matsalar ta’addanci da ayyukan masu tsattsauran ra’ayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM