
Mutane 1,430 sun mutu, 3,238 sun jikkata sakamakon girgizar ƙasa a Venezuela
Adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar ƙasa a ƙasar Venezuela ya kai 1,430, yayin da mutane 3,238 suka jikkata.
Masu kashe gobara daga ƙasar Argentina na ci gaba da laluben waɗanda ake zargin sun maƙale a ƙarƙashin wani gini da ya rushe a yankin Caraballeda na jihar La Guaira, bayan girgizar ƙasa biyu da suka afku a ranar 27 ga Yuni, 2026.
A cewar rahotanni, miliyoyin mutane na fuskantar ƙarancin tsaftataccen muhalli da sauran muhimman buƙatu na rayuwa, yayin da jiragen farko na tallafin agajin gaggawa daga Amurka suka sauka a birnin Caracas.
Shugaban Majalisar Dokokin Venezuela, Jorge Rodríguez, ya bayyana a ranar Asabar cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon girgizar ƙasar ya kai akalla 1,430.
Rahoton CNN ya ce Rodríguez ya kuma bayyana cewa mutane 3,238 sun jikkata, yayin da iyalai 3,142 suka rasa gidajensu.
Ya ƙara da cewa, bayan manyan girgizar ƙasa biyun, an samu ƙarin girgizar ƙasa (aftershocks) har sau 430 a sassa daban-daban na ƙasar.