Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta shigar da ƙarar wasu mutum uku da ake zargi da hannu a sace ɗalibai da malamai daga wasu makarantu a ƙaramar hukumar Oriire ta Jihar Oyo.
A cikin tuhumar mai ƙunshe da laifuffuka guda 10 da aka shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, gwamnati ta zargi Abdulrazak Umar (wanda aka fi sani da Abu Khalifa ko Abu Khalid), Yunusa Musa (Yunusa bin Musa) da Shamsu Adamu Sani (Abu Itisar) da laifuffuka da suka haɗa da ta’addanci, garkuwa da mutane, ɓoye bayanai, tunzura mutane da kuma haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Bisa ga takardar tuhumar, ana zargin mutanen uku, waɗanda dukkansu ‘yan ƙaramar hukumar Suleja ta Jihar Neja ne, da haɗa baki da wasu mutum uku—Muhammad Sani, Jibril Mohammed da Ibrahim Khabab—tsakanin watan Janairu da Mayun 2026 domin sace ɗaliban da malamansu a Oriire.
Har ila yau, gwamnati ta zarge su da taimakawa wajen aiwatar da satar, tare da ɓoye bayanai game da waɗanda ake zargin suka shirya harin, duk da cewa suna da masaniya kan shirin.
Haka kuma, ana zargin mutanen ukun da kasa sanar da hukumomin tsaro bayanan da suka sani game da waɗanda ake zargi da kuma shirin sace ɗaliban, lamarin da gwamnati ta ce ya saɓa wa tanade-tanaden Dokar Hana da Yaƙi da Ta’addanci ta 2022.