Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta ce ta ceto mutane 32 da aka yi garkuwa da su tare da dakile wani shirin kai harin ‘yan bindiga a kauyen Maikujera da ke karamar hukumar Rabah ta jihar.
Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakinta, DSP Ahmad Rufai, ya fitar, inda ta ce lamarin ya faru ne bayan da jami’in ‘yan sanda na ofishin Rabah (DPO) ya samu kiran gaggawa da misalin karfe 8:30 na safe, kan yadda wasu gungun ‘yan bindiga dauke da makamai suka shiga yankin.
Sanarwar ta ce ‘yan bindigar, wadanda suka gudanar da ayyukansu a wani kauye mai nisa da ke iyaka da jihar Zamfara, suna tafiya ne da dabbobin da suka sace tare da wasu mutane da suka yi garkuwa da su, yayin da suke ta harbe-harbe kan mai uwa da wabi.
Bayan samun bayanan sirri, DPO na Rabah ya tattara jami’an rundunar na musamman da suka hada da sashen yaki da garkuwa da mutane da kuma runduna ta musamman tare da hadin gwiwar sansanin sojojin da ke kusa, inda suka kafa shingaye a hanyoyin fita daga kauyen domin hana ‘yan bindigar tserewa da wadanda suka kama.
Rundunar ta ce jami’an tsaro sun yi arangama da ‘yan bindigar tare da yin musayar wuta da ya dauki lokaci mai tsawo, inda karfin makamai da dabarun jami’an tsaro suka tilasta wa ‘yan bindigar barin wadanda suka yi garkuwa da su da kuma dabbobin da suka sace, suka tsere zuwa cikin daji.
Bayan fafatawar, jami’an tsaro sun gudanar da bincike a cikin daji da yankunan da ke kewaye domin gano wadanda suka gudu domin neman mafaka.
Rundunar ta ce an samu nasarar ceto mutane 32 ba tare da sun samu rauni ba, wadanda suka kunshi maza 6 da mata 26, akasarinsu yara.