Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama wasu da ake zargi da hannu a laifukan kisan kai da rikicin Kasuwar Gujungu da ya haddasa asarar rayuka da barnar dukiya.
A Ringim, an kama Saminu Ibrahim (20) bisa zargin kashe wani matashi bayan ya daba masa ƙarfen danbuda sakamakon saɓani.
Haka kuma, ‘yan sanda sun kama mutane biyu da ake zargi da hannu a harin da aka kai wa ofishin ‘yan sanda da kona shaguna bayan rikicin da ya biyo bayan mutuwar wani matashi da ake zargin wani soja ya daba wa wuƙa a Kasuwar Gujungu.
Bugu da ƙari, an sake kama mutum shida da ake zargi da kashe wani jami’in sintiri (Vigilante) tare da jikkata wani yayin rikicin. Rundunar ta kuma ƙwato shanu shida da aka yi watsi da su a lokacin tarzomar.
Rundunar ta ce bincike na ci gaba, yayin da aka fara tattaunawa da shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki domin hana sake faruwar irin wannan rikici.
Kwamishinan ‘Yan Sanda ya tabbatar da cewa za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a laifi, tare da kira ga jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai.