Rundunar ‘ƴansanda a jihar Benue ta kama ‘yan Pakistan biyar da wayoyin hannu guda 35 a yayin wani samame daban-daban da jami’an leƙen asiri suka kai a Otukpo da Ugbokolo.
Kakakin rundunar, DSP Aondongu Orchia, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar,inda ya bayyana cewa an kama uku daga cikin wadanda ake zargin a ranar 4 ga Agusta a Adoka Motor Park, karamar hukumar Otukpo, yayin da suke yunkurin hawa mota zuwa kauyen Adoka.
Ya bayyana sunayensu a matsayin Younas Mohammad, mai shekaru 36; Ahmad Nunil, mai shekaru 38; da Aslam Muhammad, mai shekaru 46.
A cewarsa, wadanda ake zargin sun yi ikirarin cewa suna Otukpo ne don tallata kayan kwalliya da na’urorin hannu, amma babu daya daga cikin kayayyakin da aka samu a hannunsu.
Orchia ya ce an kama wasu ‘ƴan Pakistan biyu, Juma Sharif, mai shekaru 30, da Muhammed Sharif, mai shekaru 25, a ranar 5 ga Agusta a wani otal na yankin da ke Ugbokolo.
Ya ce wadanda ake zargin biyu sun yi ikirarin cewa dillalan wayoyin android ne, inda ya kara da cewa binciken kayansu ya haifar da kwato wayoyin Tecno Camon 50 Pro guda 11.
Ci gaba da bincike da kuma bin diddigin aiki ya haifar da kwato wasu wayoyin Tecno Camon 50 Pro guda 23 da kuma wayar Infinix Hot 60 guda daya,” in ji shi.
Orchia ya ce an tura wadanda ake zargin guda biyar zuwa sashen binciken laifuka na Jiha (SCID), Makurdi, domin ci gaba da bincike.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ya ce rundunar ta yi zargin cewa mallakar wayoyin na iya zama dabara ga ayyukan sirri a yankunan karkara na jihar.
Ya kara da cewa wadanda ake zargin suna da wahalar magana ko fahimtar Turanci, wanda hakan ya kara haifar da cikakken bincike.
Orchia ya ce ayyukan sun kasance wani bangare na dabarun ‘yan sanda na hukumar na gano barazanar tsaro, hana ayyukan laifuka da kuma kare rayuka da dukiyoyi.