Tsohon Gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027, Peter Obi, ya ziyarci al’ummomin Otukpo-Nobi da Efeyi-Ugboju da ke Ƙaramar Hukumar Otukpo ta Jihar Benue, waɗanda hare-haren ’yan bindiga suka shafa.
Obi ya ce yayin ziyarar, ya samu labarin cewa sama da mutum 10 ne aka kashe ko suka ɓace a Otukpo-Nobi, yayin da wasu da dama suka samu raunuka tare da kwantar da su a asibiti.
Ya kuma ce sama da mutum 13 aka ruwaito an kashe a Efeyi-Ugboju, inda ya halarci wurin da aka binne wasu daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu, tare da yi wa iyalansu ta’aziyya.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Obi ya kuma ziyarci asibiti domin duba waɗanda suka jikkata tare da yi musu fatan samun sauƙi. Ya ce an kuma sanar da shi cewa ’yan bindiga sun sace mutane 14 a kan hanyar Ankpechi da safiyar ranar da ya kai ziyarar.
Obi ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya, yana mai cewa babban nauyin gwamnati shi ne tabbatar da tsaro da jin daɗin al’ummarta.