‘Yan takara 19 ne aka jera sunayensu domin fafatawa a zaben gwamnan Jihar Sokoto na shekarar 2027, kamar yadda jerin sunayen da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta wallafa a ofishinta da ke Sakkwato ya nuna.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa jerin sunayen, wanda wakilinta ya gani yayin ziyartar ofishin hukumar a ranar Asabar, ya kunshi ‘yan takara daga jam’iyyun siyasa daban-daban da ke neman kujerar gwamnan jihar.
Daga cikin jam’iyyun da aka jera akwai Action Alliance, Social Democratic Party, Action Peoples Party, Action Democratic Party, Allied Peoples Movement, Zenith Labour Party, All Progressives Grand Alliance, Peoples Redemption Party, New Nigeria Peoples Party, National Rescue Movement, African Action Congress, Accord, Young Progressives Party, National Democratic Party, Labour Party, National Democratic Congress, Peoples Democratic Party da All Progressives Congress.
Daga cikin wadanda aka jera akwai Aliyu Shamsudeen Ahmad na NDC, Abdullah Sokoto Abubakar na PDP, Manir Muhammad Dan’Iya na ADC da kuma gwamnan jihar mai ci, Ahmed Aliyu Sokoto, wanda ke takarar karkashin jam’iyyar APC.
Yawaitar ‘yan takarar na zuwa ne yayin da ake kara fuskantar shirye-shiryen siyasa gabanin zaben na 2027, inda ake sa ran ‘yan takarar za su fara ko kuma kara kaimi wajen gudanar da shawarwari, neman goyon baya da sauran harkokin siyasa.
Sai dai shigar jam’iyyar PDP cikin tseren na fuskantar kalubale sakamakon rikicin cikin gida da har yanzu ba a warware ba, inda aka jera Abdullah Sokoto Abubakar a matsayin dan takarar bangaren da ke da alaka da sansanin Wike/Bature.
Sakataren Yada Labarai na daya daga cikin bangarorin PDP, Hassan Sahabi Sanyinnawal, ya ce suna nazarin halin da ake ciki, kuma za su bayyana matsayinsu ga jama’a bayan sun kammala duba lamarin.
Ya kuma yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu tare da kaucewa duk wani mataki da ka iya kara rura rikicin cikin gida na jam’iyyar.
Da ‘yan takara 19 yanzu haka, ana sa ran tseren neman kujerar gwamnan Sakkwato zai kasance mai zafi, yayin da APC, PDP, ADC da sauran jam’iyyun siyasa ke neman samun goyon bayan masu zabe a fadin jihar.