Jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta ce Shugaba Bola Tinubu ba shi da cikakken shiri da kwarewar samar da tsarin da zai magance matsalar rashin tsaro da sauran kalubalen da Najeriya ke fuskanta.
Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Abubakar Yusuf, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
Yusuf ya kuma ce gwamnan Oyo kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2027, Seyi Makinde, yana da tsarin da zai magance matsalar tsaro da sauran matsalolin kasar.
Ya soki Ministan Tsaro, Christopher Musa, kan ikirarin da ya yi cewa matsalar tsaro a Najeriya ta ragu, yana mai cewa irin wannan magana na nuna cewa gwamnatin Tinubu ba ta fahimci hakikanin halin da kasar ke ciki ba.
APM ta kuma kalubalanci shugaban kasa da jami’an gwamnatinsa da su yi tafiye-tafiye ta kasa ba tare da rakiyar jami’an tsaro ba domin su ga irin barazanar da talakawa ke fuskanta.
Jam’iyyar ta ce Najeriya ba za ta iya sake shafe wasu shekaru hudu karkashin abin da ta kira gwamnatin Tinubu mai gazawa ba, inda ta bukaci ‘yan Najeriya su zabi Makinde a zaben 2027.