Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya bayyana gwamnatin tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari a matsayin gwamnatin da ta fi kowace gwamnati cin hanci da rashawa a tarihin Najeriya.
Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin MIC On Podcast tare da Seun Okinbaloye.
An tambaye shi ra’ayinsa kan manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu, musamman cire tallafin man fetur da haɗa kasuwannin musayar kuɗaɗen waje.
Ya ce babu wata manufar tattalin arziki, komai ingancinta, da za ta yi nasara matuƙar cin hanci da rashawa ya ci gaba da samun gindin zama a cikin gwamnati.
Da yake bayyana dalilin da ya sa yake kallon gwamnatin Buhari a matsayin mai yawan cin hanci da rashawa, Baba-Ahmed ya ce cin hanci na daga cikin abubuwan da suka haddasa gazawar tsohon shugaban ƙasar wajen gudanar da mulkinsa.
Ya kuma danganta sukar da yake yi wa gwamnatin Buhari da zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, yana zargin gwamnatin da gaza cika alkawarin gudanar da zaɓe mai inganci da sahihanci.