Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya yi alkawarin rage farashin man fetur, iskar gas da man jiragen sama zuwa N200 kan lita cikin shekara guda idan aka zaɓe shi a 2027.
Adebayo ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Abuja, inda ya ce za a cimma hakan ta hanyar farfaɗo da matatun man fetur na cikin gida da kuma samar da yanayi mai kyau ga ƙananan matatun mai.
Ya kuma ce gwamnatinsa za ta dawo da tsarin tallafin man fetur na baya, inda ake ware ganga 450,000 na ɗanyen mai domin amfanin cikin gida, sannan a yi amfani da kuɗin da ake samu daga sauran sinadaran man wajen daidaita farashin.
Dan takarar ya ce muhawarar cire tallafin mai na ɗauke hankalin gwamnati daga muhimmin abin da ya kamata a mayar da hankali a kai, wato samar da isasshen ƙarfin tace ɗanyen mai a cikin Najeriya.
Adebayo ya kuma yi alkawarin inganta sufurin jama’a da layin dogo, tare da rage kuɗin sufuri da gidaje ga ma’aikata, da samar da ilimi da kiwon lafiya kyauta idan SDP ta samu nasarar kafa gwamnati.
Ya ce gwamnatin SDP za ta kuma mayar da hankali kan noma da samar da wadataccen abinci domin rage tsadar rayuwa.