NE

News Elementor

Kotu ta wanke direban Adaidaita Sahu daga zargin kisa kai a Kano

Babbar kotun jihar Kano da ke kan titin Miller Road ta wanke wani direban Adaidaita Sahu, Imran Mustapha, wanda ake zargi da kisan kai.

Mai shari’a Adam Abdullahi ne ya jagoranci shari’ar, inda ya yanke hukuncin cewa an wanke Mustapha tare da sallamarsa bayan kotun ta gano cewa ba a tabbatar da laifin da ake zarginsa da shi ba.

Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Mustapha ne bisa zargin kisan kai, ƙarƙashin sashe na 221 na kundin dokokin Penal Code. Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.

A yayin shari’ar, masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu shida domin tabbatar da zargin, yayin da lauyan kariya, Barrista Mubarak, ya gabatar da wanda ake tuhumar domin ya bayar da shaidar kansa.

Shari’ar ta samo asali ne daga zargin cewa Mustapha ya bugi motar marigayi Alhaji Muhammad Mustapha a wani gidan mai.

Rahotanni sun ce marigayin ya bi motar Mustapha bayan faruwar lamarin, lamarin da ya haifar da gardama tsakaninsu.

Masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa daga bisani Mustapha ya sake bugun Muhammad Mustapha da motarsa, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

Sai dai bayan duba hujjoji da bayanan da bangarorin biyu suka gabatar, kotun ta ce masu gabatar da ƙara sun kasa tabbatar da zargin kisan kai a matakin da doka ta tanada.

Saboda haka, kotun ta wanke Imran Mustapha tare da sallamarsa daga tuhumar kisan kai.

Sai dai lauyan gwamnati, Barrista Usman Abdullahi, ya bayyana cewa gwamnati ba ta gamsu da hukuncin kotun ba, kuma za ta daukaka ƙarar zuwa wata kotu mafi girma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM