Rahotanni sun ce an kama Mahmoud Adam, wani da ake zargin ɗan ta’adda ne wanda ake danganta shi da kashe Kiristoci a Najeriya, musamman a yankin Arewa ta Tsakiya.
Kafar yaɗa labarai ta Daily Caller da ke Amurka ce ya tabbatar da kama wanda ake zargin a wani rahoto na musamman da ta wallafa ranar Juma’a.
A cewar rahoton, Adam, wanda ke zaune a Jihar Plateau, ana zargin shi ne boyayyen jagora na wata ƙungiyar mayaƙa ta kabilar Fulani.
Wani tsohon jami’in leƙen asirin Amurka da ya ƙware a harkokin ta’addanci, wanda ya yi magana da Daily Caller, shi ma ya tabbatar da kama wanda ake zargin.
Rahoton ya yi zargin cewa wasu hotuna da wani mai fallasa bayanan sirri ya bayar sun nuna cewa wanda ake zargin ya taɓa ganawa da manyan shugabannin sojojin Najeriya tare da karɓar kyaututtuka masu daraja daga gare su, yayin da wani sanata mai ci a yanzu ya taɓa shiga tsakani domin a sake shi.
An gudanar da samamen da ya kai ga kama shi ne a ranar 12 ga Satumba, a gidansa da ke Jihar Plateau, inda ake zargin yana aiki a matsayin wani fitaccen shugaban al’ummar Fulani.