NE

News Elementor

An kama matashi kan zargin kashe wani mutum saboda bashin N500 a Jigawa

Rundunar ’yansandan Jihar Jigawa ta kama wani matashi mai shekaru 20, Lawisi Safiyanu, bisa zargin ya daba wa Muhammad Abba wuka har ya mutu sakamakon rashin jituwar da ta biyo bayan bashin N500.

A cewar kakakin rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare ranar 1 ga Oktoba, 2026, a ƙauyen Chamo da ke Ƙaramar Hukumar Dutse.

Rundunar ta ce Abba ya sayi wayar hannu daga hannun wanda ake zargin kan N1,500, inda ya biya N1,000 sannan ya rage masa N500. Ana zargin sabani ya kaure tsakaninsu kan bashin, kafin Safiyanu ya yi amfani da wuka ya caka wa Abba.

An garzaya da wanda aka raunata zuwa Asibitin Koyarwa na Rashid Shekoni da ke Dutse, amma likitoci suka tabbatar da rasuwarsa. ’Yan sanda sun ce an kama wanda ake zargin tare da kwato wukar da ake zargin an yi amfani da ita.

A wani lamari dabam, rundunar ta kuma kama Abbas Ibrahim, mai shekaru 27, bisa zargin shiga ɗakin babban ɗan’uwansa, Basiru Shuaibu, mai shekaru 25, ya zuba masa fetur sannan ya cinna wuta.

Lamarin ya jikkata Basiru da matarsa da munanan kone-kone, yayin da Basiru daga bisani ya mutu sakamakon raunukan da ya samu. An kama Abbas a garin Sara, Ƙaramar Hukumar Gwaram, kuma yanzu ana gudanar da bincike a kansa a sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) da ke Dutse.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jigawa, CP Tijjani Murtala, ya bukaci jama’a da su guji daukar doka a hannunsu, tare da sanar da jami’an tsaro duk wani rikici ko barazana cikin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM