Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama Faisal Abdulrasheed Maina, ɗan tsohon shugaban kwamitin sake fasalin tsarin fansho na ƙasa (PRTT), Abdulrasheed Maina, bayan shafe kusan shekaru shida yana gudun hijira.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa jami’an DSS sun kama Faisal a yankin Karsana da ke Abuja, bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa ya dawo Najeriya a ɓoye.
Majiyoyi sun ce an miƙa shi ga hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) bayan kama shi.
Faisal ya tsere daga ƙasar ne a shekarar 2020, bayan EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotu kan tuhume-tuhume uku da suka shafi halatta kuɗin haram, inda aka ba shi beli amma ya karya sharuddan belin.
A watan Oktoban 2021, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta same shi da laifi, tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari, duk da cewa ana ci gaba da shari’ar ba ya nan.
Alkalin kotun, Okong Abang, ya ce EFCC ta tabbatar da cewa Faisal ya yi amfani da wani asusun banki na bogi a bankin United Bank for Africa (UBA), wanda mahaifinsa ya yi amfani da shi wajen halatta kuɗi har naira miliyan 58.1.
Kotun ta bayyana cewa an fara saka kuɗin ne a asusun da aka buɗe da sunan “Alhaji Faisal Farm 2”, kafin Faisal da mahaifinsa su riƙa cire kuɗin tsakanin Oktoban 2013 da Yunin 2019.
A watan Nuwamban 2022, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Faisal, amma ta rage wa’adin ɗaurinsa daga shekaru 14 zuwa bakwai, bisa dalilin cewa bai dace kotun farko ta yanke masa hukuncin mafi tsanani ba alhali shi ne karon farko da aka same shi da laifi.
Mahaifinsa, Abdulrasheed Maina, ya yi zaman gidan yari na shekaru takwas a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja, bayan samunsa da laifin halatta kuɗaɗen fansho naira biliyan biyu.
An sako Maina a farkon shekarar 2026, amma daga baya aka ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo kan zargin karɓar kayayyakin da aka sace.