Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa Arewa za ta mara masa baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Bayanin hakan na ɗauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Yusuf ya bayyana hakan ne ranar Asabar a Abuja, yayin ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen Tinubu na ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A).
Gwamnan ya ce Kano, wadda ke da mafi yawan masu kaɗa ƙuri’a a Arewacin Najeriya, za ta jagoranci sauran jihohi wajen samar da ƙuri’u ga Tinubu, wanda ke neman wa’adi na biyu a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar A4A za ta taimaka wajen tattara goyon baya da ƙarfafa hulɗar siyasa a faɗin jihohin Arewa gabanin zaɓen 2027.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce wajibi ne a haɗa goyon bayan siyasa da riƙon amana, kyakkyawan shugabanci da samar da sakamakon da zai inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Shettima ya amince da ƙalubalen tattalin arzikin da ‘yan ƙasa ke fuskanta, yana mai jaddada buƙatar gwamnati ta mayar da hankali kan tsaro, ilimi, rage talauci da samar da hanyoyin samun ci gaba na tattalin arziki.
Ƙungiyar A4A na da manufar haɗa kan masu goyon bayan Tinubu da Shettima a jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Tsohon Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ne shugaban ƙungiyar ta A4A.