Dakarun Sojojin Najeriya sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun ceto wani mutum da aka sace, tare da kwato kuɗin fansa naira miliyan 10 a wani samame da suka gudanar a dajin Falgore, ƙaramar hukumar Doguwa ta Jihar Kano.
Dakarun Birged ta 3, ƙarƙashin Operation MESA, ne suka gudanar da samamen bayan sace Alhaji Kabiru Aliyu a ƙauyen Fanyabo da ke cikin dajin Falgore a ranar 11 ga Oktoba, 2026.
A cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojojin Birged ta 3, Manjo Babatunde Zubairu, ya fitar a ranar Asabar, ya ce an sace mutumin ne da misalin tsakar dare lokacin da yake dawowa daga kasuwar Yandoka da ke Jihar Kaduna.
Sanarwar ta ce daga bisani masu garkuwar sun tuntubi iyalan wanda aka sace a ƙauyen Yan Taburmi, wanda shi ma yake cikin dajin Falgore, inda suka nemi a biya kuɗin fansa domin sakin sa.
A cewar Sojojin, dakarunsu sun samu sahihan bayanan sirri, sannan suka shirya kwanton ɓauna tare da haɗin gwiwar ’yan sanda, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da mafarautan yankin.
Ta ƙara da cewa binciken da aka gudanar a yankin daga baya ya kai ga gano naira miliyan 10 da aka bayar a matsayin kuɗin fansa, kamar yadda aka ruwaito.
Sanarwar ta bayyana cewa an mayar da kuɗin da aka kwato ga wanda aka sace da iyalansa.
Kwamandan Birged ta 3, Birgediya Janar Saka Jimoh, ya yaba wa dakarun bisa kasancewarsu cikin shiri, ƙwarewarsu da jajircewarsu yayin gudanar da samamen.
Jimoh ya sake jaddada aniyar birged ɗin na ci gaba da matsa lamba kan masu aikata laifuka da kuma hana sake samun matsalolin tsaro a yankin.
Ya kuma buƙaci al’umma da su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci, domin tallafa wa ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Kano.