NE

News Elementor

Tinubu ya ce ba za a dawo da tallafin man fetur ba a Nigeria kamar yadda Annabi Musa ba zai koma hannun Fir’auna ba

Shugaban kasa Bola Tinubu ya jaddada cewa, ba za a dawo da tallafin man fetur ba a kasar nan, inda ya ce gwamnatinsa ta dauki matakai masu tsauri domin inganta tattalin arziki.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da kungiyar City Boy Movement, wata kungiyar matasa da aka kafa domin yada manufofin gwamnatinsa.

Ya ce ya janye tallafin man fetur ne tun a ranarsa ta farko, kuma yana jin alkawuran da yan adawa ke yi na dawo da tallafin, sai dai ya ce Nigeria za ta iya durkushewa saboda babu wasu kudi da za a yi amfani da su wajan biyan tallafin.

Da yake buga misali da batun da ya shafi addini da tarihi, Tinubu ya kafa hujja da kissar Alqurani da Bible, inda ya ce lokacin da Annabi Musa ya baro Misra, kuma Kogi ya rabu gida biyu domin ya tsallaka, to babu wanda zai iya cewa Musa ya koma Misra duk da sanin matsalar da ya baro a can.

Daga nan ya shedawa mahalarta taron cewa, tare da taimako da goyon bayansa, suma yan Nigeria ba za su koma Misrar da suka baro ta tallafin man fetur ba.

Tsohon gwamnan na jihar Legas, ya yabawa kungiyar a bisa goyon bayan da take bawa gwamnatinsa, inda ya bukaci wakillan kungiyar da su tallata nasarorin da ya samar ga alummar Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM