Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya ce sake dawo da tallafin man fetur a Najeriya zai ƙara tsananta talauci tare da rage sha’awar masu zuba jari a ƙasar.
Mbah ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wani taron tattaunawa da ’yan takarar siyasa da Afia TV ta shirya a Enugu, inda ya kare matakin Shugaba Bola Tinubu na cire tallafin man fetur.
Gwamnan ya ce Najeriya ba za ta iya komawa tsarin tallafin mai ba, yana mai cewa hakan zai iya jawo faduwar darajar naira da kuma firgita masu zuba jari.
Ya ce maimakon sake dawo da tallafin, ya kamata gwamnati ta mayar da hankali wajen tabbatar da cewa al’umma sun amfana da kuɗaɗen da aka samu daga cire shi, ta hanyar samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.
Mbah ya kuma ce tsarin tallafin man fetur ya fi amfanar masu kuɗi, yayin da gwamnatin tarayya ke amfani da kuɗaɗen da ta samu daga cire tallafin wajen tallafa wa marasa galihu, ciki har da shirin bayar da tallafin kuɗi da jari ga mutum 1,000 a kowace mazaba a faɗin ƙasar.
Ya ƙara da cewa manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu sun taimaka wajen daidaita wasu muhimman alamomin tattalin arziki da ƙara jawo masu zuba jari na cikin gida da na ƙasashen waje.
A wani ɓangare, gwamnan ya lissafa wasu ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar, ciki har da kafa makarantu masu fasahar zamani guda 268, cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko guda 260, kamfanin jirgin sama na Enugu Air da motocin bas masu amfani da iskar CNG.
Ya ce idan aka sake zaɓensa, gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan inganta ilimi, gina hanyoyi, samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 660, kafa tsarin jirgin ƙasa na monorail da kuma fara zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa da ƙasa daga Enugu.