NE

News Elementor

Akwai buƙatar gwamnatin Sokoto ta ɗauki matakan gaggawa da inganta tsaro a faɗin jihar – Manir Ɗan’iya

Ɗan takarar gwamnan jihar Sokoto na jam’iyyar ADC, Hon. Manir Muhammad Dan’iya, ya bayyana alhini kan sabon harin ’yan bindiga da ya auku a jihar, inda aka kashe Babban Limamin ƙauyen Talluje da wasu mutum biyu a ƙaramar hukumar Bodinga.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Aminu Abdullahi, ya fitar, Dan’iya ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, al’ummar ƙauyen Talluje, Ƙaramar Hukumar Bodinga da daukacin al’ummar Jihar Sokoto.

Ya ce harin, wanda rahotanni suka ce ya yi sanadin sace wasu mutane tare da raba daruruwan mazauna yankin da muhallansu, ya sake nuna bukatar ɗaukar matakan gaggawa da inganta tsaro a faɗin jihar.

Dan’iya ya bayyana cewa ci gaba da hare-haren da ake kai wa al’ummomi na haifar da fargaba, durƙusar da harkokin tattalin arziki da kuma tilasta wa iyalai da dama barin gidajensu.

A cewarsa, wajibi ne gwamnati ta ba da fifiko wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, domin ba za a samu ci gaba mai ɗorewa ba idan jama’a ba su da zaman lafiya.

Ya buƙaci Gwamnatin jihar Sokoto ta ƙara haɗa kai da hukumomin tsaro na tarayya, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da ingantattun hanyoyin magance matsalar tsaro.

Haka kuma ya roƙi hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri, ƙarfafa sintiri a yankunan da ke fuskantar barazana, tare da tabbatar da cafke masu hannu a hare-haren domin su fuskanci hukunci.

Dan’iya ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai, tare da gujewa duk wani abu da ka iya kawo cikas ga ayyukan tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM