Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗaya daga cikin gwamnatoci mafi muni a tarihin Najeriya.
A cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, Daraktan Kamfen ɗin Shugaban Ƙasa na jam’iyyar ADC, ya fitar a madadinsa, Atiku ya zargi Tinubu da jefa rayuwar yan ƙasa cikin ƙunci.
Atiku ya ce ba za a iya ware batun bashin daga abin da ya bayyana a matsayin ƙara faɗaɗa tazara tsakanin ikirarin gwamnati na farfaɗowar tattalin arziki da kuma halin da talakawan Najeriya ke ciki ba a rayuwarsu ta yau da kullum.