
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya naɗa ɗan siyasa kuma jarumin fina-finai, Kenneth Okonkwo, a matsayin kakakinsa na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
A cikin wasiƙar naɗin, Atiku ya bayyana cewa ya zaɓi Okonkwo ne bayan ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), yana mai yabawa ƙwarewarsa, nagarta da iya isar da saƙon yaƙin neman zaɓe.
Da yake martani, Okonkwo ya gode wa Atiku bisa amincewar da ya yi da shi, yana cewa naɗin ya nuna irin salon shugabancin Atiku na tattaunawa da neman mafita. Ya kuma ce tattaunawar da aka yi a cikin ADC ta tabbatar da kare muradun yankin Kudu maso Gabas.
A baya, Okonkwo ya kasance kakakin yaƙin neman zaɓen Peter Obi a zaɓen 2023, sai dai daga baya rikici ya shiga tsakaninsu. Atiku kuwa zai sake neman kujerar shugaban ƙasa a karo na bakwai a zaɓen 2027.