NE

News Elementor

Gwamnan Kano Abba Kabir, Ya Buƙaci Kanawa Su Ci Gaba Da Goyon Bayan Gwamnatin Tinubu

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci al’ummar jihar da su ci gaba da mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya, yana mai cewa shugaban ya cancanci samun cikakken goyon baya saboda irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban Kano da Najeriya baki ɗaya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Gwamna Abba ya yi wannan kira ne yayin da yake miƙa takardar shaidar nasara ga sabon ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Dawakin Kudu/Warawa, Hon. Shu’aibu Rabi’u Nagogo (Abba Gano), a Fadar Gwamnatin Kano.

Gwamnan ya ce al’ummar Kano na da dalilai masu yawa na ci gaba da goyon bayan Shugaba Tinubu gabanin zaɓen shekarar 2027, yana mai jaddada cewa kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Gwamnatin Kano da Gwamnatin Tarayya ta samar da muhimman ayyukan ci gaba a jihar.

Ya yabawa Shugaba Tinubu kan goyon bayan da yake bai wa manyan ayyukan more rayuwa da sauran shirye-shiryen ci gaba a Kano, tare da bayyana shi a matsayin jagoran da ke aiki domin haɗin kan ƙasa da ci gabanta.

Haka kuma, Gwamna Abba ya yi kira ga shugabannin siyasa, masu ruwa da tsaki da magoya baya da su ci gaba da haɗa kai domin ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin Kano da Gwamnatin Tarayya.

Ya kuma taya Hon. Shu’aibu Rabi’u Nagogo murnar nasarar da ya samu a zaɓen cike gurbi, yana mai bayyana kwarin gwiwarsa cewa zai wakilci al’ummar Dawakin Kudu da Warawa yadda ya kamata.

Gwamnan ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da aiki tare da Gwamnatin Tarayya wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM