NE

News Elementor

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta raba wa hukumomin tsaro motoci domin yaƙi da matsalar tsaro

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta raba motocin aiki ga hukumomin tsaro daban-daban a jihar a wani mataki na ƙara ƙarfafa yaƙi da ‘yan bindiga da sauran nau’ikan laifuffuka a faɗin jihar.

An sayo motocin ne a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmad Aliyu domin ƙara ƙarfafa wa hukumomin tsaro wajen gudanar da ayyukansu da kuma inganta tsarin tsaro a faɗin jihar.

Yayin da yake miƙa makullan motocin, Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Idris Muhammad Gobir, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin na tabbatar da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a jihar.

Ya buƙaci hukumomin tsaron da suka amfana da motocin da su yi amfani da su yadda ya kamata wajen sauke nauyin da ke kansu domin tabbatar da an cimma manufar da aka sanya a gaba.

Alhaji Idris Muhammad Gobir ya kuma jaddada cewa tabbatar da zaman lafiya da tsaro alhakin kowa ne, yana mai cewa hukumomin tsaro kaɗai ba za su iya magance matsalolin tsaro yadda ya kamata ba sai tare da cikakken haɗin kan al’umma ba.

Don haka, ya yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da ba hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar gaggauta kai rahoton duk wani mutum ko motsi da suke zargi domin ɗaukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM