NE

News Elementor

INEC ta yi watsi da takardun takarar Jonathan da PDP ta miƙa mata

Duk da ruruwar rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar PDP, shugabancin jam’iyyar tsagin Kabiru Turaki a jiya Juma’a ya sanar da miƙa sunan Goodluck Jonathan da sauran ƴan takarar da zasu tsaya ƙarƙashin jam’iyyar yayin babban zaɓe na 2027 ga hukumar zaɓen.

Tsagin na Turaki ya bayyana cewa hannu da hannu ne ya miƙawa INEC takardun takarar na Jonathan dana sauran mambobin jam’iyyar.

Sai dai shugabar sashen wayar da kai kan zaɓe na hukumar ta INE Victoria Eta-Messi ta shaidawa manema labarai a safiyar yau Asabar cewa INEC ba zata amince da takarar da aka miƙa mata takardu hannu-da-hannu maimakon bi ta shafinta da ta buɗe ba.

A jawabinta gaban manema labarai, ta ce akwai buƙatar jam’iyyu su sani cewa INEC zata mutunta bayanan ƴan takara ne kaɗai idan an shigar da su a shafinta da ta buɗe don yin rijista.

Sai dai sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ta PDP tsagin Turaki kwamared Ini Ememobong ya shaidawa manema labarai cewa INEC ta ƙi amincewa da basu damar yin rijistar ƴan takararsu a shafin da ta buɗe duk kuwa da yunƙurin da suka riƙa yi a lokuta da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan kallon masu sukar ta a matsayin makiya

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta daina kallon duk masu sukar manufofinta a matsayin makiyan Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta rika karɓar suka mai ma’ana. Sanusi ya bayyana haka ne yayin wani taron shugabanci na Oxford Global Think Tank Leadership Conference da aka...

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM