
Ƙungiyar Likitocin masu neman ƙwarewa a asibitin koyarwa ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, a wannan Juma’a, sun bayyana goyon bayansu ga yajin aikin gama-gari na sai baba-ta-gani da Ƙungiyar Likitocin masu neman ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta ayyana, wanda zai fara daga ranar Litinin, 12 ga Janairu, 2026.
An ba da rahoton cewa matakin ya biyo bayan zargin gwamnati da gaza cika muhimman yarjejeniyoyi da aka ƙulla da suka shafi jin daɗin ma’aikata da na horaswa.
An yanke wannan shawara ne bayan taron gaggawa na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa na NARD da aka gudanar ta yanar gizo a ranar 2 ga Janairu, domin duba matakin aiwatar da Yarjejeniyar Fahimta (MoU) da aka kulla da Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma’aikatun Lafiya da Kwadago.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a Sokoto a ranar Juma’a, Ƙungiyar Likitocin masu neman ƙwarewa reshen UDUTH, ta ce bitar da aka yi ta gano “gazawa sosai” daga bangaren gwamnati wajen cika muhimman alkawura.
Daga ciki har da rashin dawo da likitoci biyar da aka sallama daga Asibitin Koyarwa ta Tarayya da ke Lokoja da rashin biyan bashin karin girma da albashi da suka taru da dai sauransu.