Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta ce aƙalla mutane 10,217 ne aka kashe a hare-haren ƴan bindiga a jihohin Benue, Niger, Katsina, Kebbi, Plateau, Sokoto da Zamfara, cikin shekaru biyu na farko na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta wallafa a Facebook ranar Litinin, Amnesty ta ce Jihar Benue ce ke da mafi yawan adadin waɗanda aka kashe, sai kuma Jihar Plateau, inda mutane 2,630 suka rasa rayukansu.
Ta ce yanzu sama da shekaru uku kenan tun lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki, inda ya yi alkawarin inganta tsaro
Sai dai maimakon hakan, al’amura sun ƙara taɓarɓarewa, yayin da hukumomi ke ci gaba da gazawa wajen kare haƙƙin rayuwa, mutunci na jiki, ƴanci da kuma tsaron dubban mutane a faɗin ƙasar,” in ji Amnesty.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa cikin shekaru biyu na farko na gwamnatin, sabbin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai sun samu iko a wasu yankuna.
Amnesty ta ambaci Lakurawa a jihohin Sokoto da Kebbi, da kuma Mamuda a Jihar Kwara. Ta ƙara da cewa ƴan bindiga sun kori mazauna ɗaruruwan ƙauyuka a jihohin Benue, Borno, Katsina, Sokoto, Plateau da Zamfara.
Amnesty ta yi gargadin cewa ƙaruwa da hare-haren na haifar da barazanar bullar babbar matsalar jin kai.
Ta kuma kawo misalin gundumar Dangulbi a Jihar Zamfara, inda ta ce manoma suna kallon amfanin gonakinsu na dankalin turawa yana rubewa, saboda ƴan bindiga sun hana su kai amfanin gonar zuwa kasuwar da ta fi kusa da su.
Ƙungiyar ta ce bisa dokokin haƙƙin bil’adama na ƙasa da ƙasa, hukumomi suna da alhakin kare rayukan jama’a, tabbatar da cewa an gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata kisan, tare da tabbatar da cewa waɗanda abin ya shafa sun samu damar neman adalci da kuma ingantattun hanyoyin samun diyya.